Najeriya Ce Ke da Mafi Yawan Jiragen Sama Masu Zaman Kansu a Afirka – Keyamo

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Najeriya ce ke da mafi yawan jiragen sama masu zaman kansu (Private Jets) a nahiyar Afirka.

Keyamo ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar aiki da tawagar gwamnatin tarayya ta kai birnin Montréal na ƙasar Canada, inda suka gana da manyan kamfanonin ƙera jiragen sama na duniya domin ƙarfafa haɗin gwiwa da bunƙasa harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya.

Ya ce yawan jiragen sama masu zaman kansu da Najeriya ke da su wata babbar dama ce da za a yi amfani da ita wajen jawo sabbin zuba jari, sauƙaƙa sayen sabbin jirage, inganta tsaro, da ƙara ƙarfin kamfanonin jiragen sama na cikin gida.

A cewarsa, manufar gwamnatin tarayya ita ce haɗa masu gudanar da harkokin jiragen sama na Najeriya kai tsaye da manyan kamfanonin ƙera jirage kamar Boeing, Airbus, Embraer da Bombardier, domin sabunta jirage, inganta ayyuka da tabbatar da dorewar fannin sufurin jiragen sama.

Wakiliya ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen bunƙasa gyaran jiragen sama (MRO), horas da matuka da injiniyoyi, haɓaka fasaha da kuma mayar da Najeriya cibiyar harkokin sufurin jiragen sama a nahiyar Afirka.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img