Nafiu Bala ya ce wannan mataki na nuna ƙudurin tsaginsa na kare muradun waɗanda ya kira "mambobin asali da na gado" na jam'iyyar, tare da jaddada cewa ADC ƙarƙashin jagorancinsa za ta tsayar da 'yan takara nagari domin samar da shugabanci nagari ga 'yan Najeriya.