“Muna sanya hijabi ne domin ɓadda kamanni idan mun fita satar yara” – Kiristoci mata da ake zargi da satar yara sun amsa laifinsu bayan sake kama su a Abuja
Daga Wakiliya
Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta sake kama wasu mata biyu kiristoci da ake zargi da satar yara, bayan da suka sake komawa aikata laifin bayan sun yi zaman gidan yari na tsawon watanni huɗu.
Matan, Blessing John da Rose David, ’yan asalin jihohin Benue da Enugu ne, kuma suna zaune ne a Abuja.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a ranar Laraba yayin da take gabatar da waɗanda ake zargin.
Ta ce an fara kama matan ne a shekarar 2023 bisa zargin satar yara huɗu a yankunan Dei-Dei da Lugbe.
A cewar rundunar, an samu nasarar ceto biyu daga cikin yaran, ciki har da tagwaye, yayin da aka sayar da sauran biyun ga wasu mutane a Fatakwal kan naira miliyan 1.5 kowanne.
“An kai su kotu, kuma suka yi watanni huɗu a Kuje. Bayan sun gama zaman gidan yari, sai suka koma suka sace wannan ƙaramar yarinyar,” in ji Josephine Adeh.
Sanya hijabi wajen satar yara
Rundunar ta ce ɗaya daga cikin hanyoyin da matan ke amfani da su wajen ɓoye kansu yayin satar yaran shi ne sanya hijabi.
Josephine Adeh ta ce duk da cewa Blessing Kirista ce ’yar asalin Benue, tana sanya hijabi domin gudanar da ayyukan satar yaran.
Ta ce suna amfani da wannan sutura ne wajen ɓoye kamanninsu yayin da suke satar yara da iyayensu suka aike su ko suka tura su wani wuri.
A yayin bincike, Rose David ta amsa cewa ta shafe watanni huɗu a gidan yari kafin ta sake komawa aikata laifin.
Da aka tambaye ta wacece ta shigar da Blessing cikin lamarin, Rose ta ce:
“Wata mata ce ta shigar da ni. Eh, ni ce na shigar da Blessing.”
“An haife ni kuma na taso a Kano”
Blessing John, wadda ba ta yi zaman gidan yari ba a shekarar 2023 saboda an yi mata tiyata makonni biyu kafin faruwar lamarin, ita ma ta amsa cewa ta shiga cikin lamarin.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa take sanya hijabi alhali ita Kirista ce, sai ta ce:
“An haife ni kuma na taso a Kano.”
Blessing ta fashe da kuka yayin da take magana kan abin da ta aikata.
Dukkan matan biyu na da aure da ’ya’ya, kuma sun nemi a yafe musu, suna cewa iyalansu ba za su ji ɗaɗin abin da suka aikata ba.
Rundunar ’yan sandan ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Ta kuma yi kira ga mazauna Abuja da su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani abin da suka gani da ya shafi laifi.
“Idan ka ga wani abu, ka faɗa. Haka kuma ga iyaye mata: Ku kula da yaranku. Kada ku tura yara waje ba tare da wani babba ya raka su ba,” in ji Josephine Adeh




