2027: Ina cikin matsala, don na san idan Atiku ko Obi suka kayar da Tinubu, da ni za su fara — Wike
Daga Wakiliya
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce yana ganin zai kasance mutum na farko da za a far wa idan Shugaba Bola Tinubu ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Wike ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya ce yana sane da haɗarin siyasar da yake yi. Shi yasa a yanzu babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa.
“Kowace rana idan zan kwanta, ina tunanin sake zaɓen shugaban ƙasa. Idan ina cin abinci, ina tunanin sake zaɓensa. Duk abin da nake yi yanzu ya shafi sake zaɓen shugaban ƙasa ne.” – a cewar ministan




