Kisan Gilla a Maraban Jos: An Gurfanar da Mutum 24, Sama da 100 Na Fuskantar Bincike

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gurfanar da mutum 24 a gaban Kotun Majistare da ke NDA Junction, Kaduna, bisa zarginsu da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata a Maraban Jos.

Ana tuhumar wadanda ake zargin da hada baki wajen aikata laifi, tayar da tarzoma, lalata kadarorin jama’a da na ’yan sanda, da kuma kisan kai.

Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Yuni, 2026, lokacin da wasu fusatattun matasa suka kwace matar daga hannun ’yan sanda tare da kashe ta.

Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga Yuli, 2026, tare da umartar a tsare duk wadanda ake tuhuma a gidan gyaran hali har zuwa lokacin ci gaba da shari’ar.

Rundunar ta ce har yanzu tana binciken sama da mutum 100 da ake zargin suna da hannu a lamarin, tare da jaddada cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bisa doka.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Muhammad Rabiu, ya yi alkawarin tabbatar da an yi wa mamaciyar adalci, tare da gargadin jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.

Er2eŕ

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img