Amurka Ta Saka Sunan Dan Najeriya Da Kamfanonin Canjin Kudi Uku Cikin Masu Daukar Nauyin ISIS

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Gwamnatin Amurka ta sanya sunan wani dan Najeriya, Mukhtar Adamu Muhammad, da kuma kamfanoni uku na canjin kudi da ke aiki a Najeriya cikin jerin mutanen da take zargi da taimakawa harkokin kudaɗen kungiyar ta’addanci ta ISIS.

A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, an zargi Mukhtar Adamu da amfani da kamfanonin canjin kudi wajen sauƙaƙa zirga-zirgar kudaden da ake dangantawa da ISIS a Yammacin Afirka.

Kamfanonin da aka ambata sun hada da Generation Currency Bureau De Change Limited da Nine to Nine Exchange Bureau De Change Limited a Lagos, sai kuma Manhattan Bureau De Change Limited da ke Kano.

Amurka ta ce matakin wani bangare ne na kokarinta na dakile hanyoyin samun kudaden kungiyoyin ta’addanci a duniya, tare da jaddada ci gaba da hadin gwiwa da Najeriya wajen yaki da ta’addanci.

Hukumar ta bayyana cewa matakin ya shafi mutane uku da kamfanoni shida daga kasashe daban-daban, ciki har da Najeriya, Faransa, Siriya da Turkiyya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img