Kotu Ta Ƙi Sauƙaƙa Sharuɗɗan Belin El-Rufai, ta dage shari’ar zuwa Satumba 22

DA DUMI-DUMI

Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da buƙatar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na sauya sharuɗɗan belinsa a shari’ar da ake masa kan zargin satar bayanan sirri ta hanyar na’urorin sa ido.

Lauyoyin El-Rufai sun nemi a sassauta sharuɗɗan belin da suka haɗa da gabatar da masu tsaya masa da ke mataki na 17 a aikin gwamnati, masu kadarori a Maitama ko Asokoro, tare da wasiƙar tabbatarwa daga Majalisar Sarakunan Kaduna. Sai dai kotun ta ce akwai masu iya cika waɗannan sharuɗɗa, don haka ta ƙi amincewa da buƙatar.

A zaman kotun na yau, Hukumar DSS ta sanar da kammala gabatar da shaidunta, inda lauyan gwamnati Oluwole Aladedoye ya bayyana cewa ba za su sake kiran wani shaida ba.

A nasa ɓangaren, lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, ya ce za su gabatar da bukatar “no-case submission”, wato neman kotu ta wanke wanda ake tuhuma saboda rashin isassun hujjojin tuhuma.

Kotun ta bai wa ɓangarorin biyu makwanni biyu domin gabatar da takardunsu, sannan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 22 ga Satumba, 2026, domin sauraron bukatar da kuma ci gaba da shari’ar.Kanun Labari: Kotun Tarayya Ta Ƙi Sauƙaƙa Belin El-Rufai, DSS Ta Rufe Shari’arta

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img