Gwamnatin Tarayya ta rage harajin shigo da motoci, ‘yan kasuwa na jiran karin bayani kan Green Tax

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da sabon tsarin rage harajin shigo da motoci a karkashin matakan kasafin kudin 2026.

Sabon tsarin ya rage harajin shigo da sabbin motoci daga kashi 20 zuwa kashi 10, yayin da na tsofaffin motoci ya sauka daga kashi 15 zuwa kashi 5.

Sai dai gwamnatin ta kuma bullo da wani sabon haraji mai suna Green Tax, wanda aka ce an kirkiro shi domin kare muhalli.

Shugaban Ƙungiyar Masu Dillancin Motoci ta Kasa, Prince Ajibola, ya ce matakin rage harajin abin a yaba ne, amma har yanzu ba za a iya tabbatar da ko farashin motoci zai sauka ba har sai gwamnati ta bayyana adadin Green Tax.

Ya bayyana cewa idan sabon harajin bai yi yawa ba, masu sayen motoci za su amfana da raguwar farashi. Amma idan Green Tax ya yi daidai ko ya fi adadin da aka rage, to ba zai kawo wani gagarumin sauyi ba.

Masu ruwa da tsaki a bangaren motoci na sa ran Hukumar Kwastam za ta yi karin haske kan yadda za a aiwatar da sabon harajin domin a tantance tasirinsa ga farashin motoci a Najeriya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img