Kotun Tarayya Ta Tabbatar da David Mark a Matsayin Halastaccen Shugaban ADC

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da halaccin shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, tare da yin watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar yana ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar.

Mai shari’a Musa Liman ya ce kotu ba ta da hurumin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyya, sannan ya bayyana cewa Abejide bai bi hanyoyin sasanta rikici na cikin jam’iyyar ba kafin ya garzaya kotu.

Kotun ta kuma yanke cewa naɗin David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar da kuma Rauf Aregbesola a matsayin sakatare ya gudana ne bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma Dokar Zaɓe ta 2026.

Haka kuma, kotun ta ci tarar Abejide Naira miliyan 2 ga kowane ɗaya daga cikin waɗanda ya ƙara, sannan ta ci lauyansa Naira miliyan 10 saboda shigar da ƙarar.

Abejide dai ya nemi kotu ta soke mika ragamar shugabancin ADC daga tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, zuwa David Mark da Aregbesola, tare da hana INEC amincewa da su, amma kotu ta yi fatali da dukkan buƙatunsa.

Wakiliya | Muryar Arewa a Duniya

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img