Wani ɗan gwagwarmaya a Kano ya yi alkawarin Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya kawo hujjar amfanin cire tallafin mai ga Talakan Najeriya
Daga Wakiliya
Wani ɗan gwagwarmaya a Kano, Dr Usman Muhammad Abdulhamid, ya yi alkawarin ba da Naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya iya kawo hujjar wasu nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Dr Abdulhamid, wanda shi ne shugaban wata ƙungiya a Kano, (KFIPM), ya ce ya shirya bayar da kuɗin ne domin ƙalubalantar masu goyon bayan gwamnatin kan manufofin cire tallafin man fetur da kuma ayyukan gwamnatin tarayya a Kano.
A wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, ya ce ya raba kyautar zuwa gida biyu, inda zai bayar da Naira 500,000 kan kowace tambaya.
Tambayarsa ta farko ita ce: Wane amfani kai tsaye talakan Najeriya yake samu a yau sakamakon cire tallafin man fetur?
Sai tambaya ta biyu, inda ya nemi a nuna masa wani aiki da ya kai darajar Naira biliyan 10 a Kano, wanda gwamnatin Shugaba Tinubu ta ƙirƙira, ta fara, ta kammala a wannan wa’adin mulkinta.
Ya ce duk wanda ya iya amsa tambayoyin biyu tare da gabatar da hujjojin da za a iya tantancewa, zai ba shi Naira miliyan ɗaya nan take.
Dr Abdulhamid ya ce yanzu mutane ba sa gamsuwa da taken siyasa da waƙoƙin kamfen kawai, inda ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta nuna abin da ta yi da zai sa jama’a su sake zaɓenta a 2027.
Ya ce, “Ku ba mu dalilin da ya sa za mu sake zaɓar wannan gwamnati. Mutane ba sa saurin ruɗuwa yanzu. Ba za ku sa su zaɓe ku da waƙoƙin kamfen kawai ba. Dole ku ba su dalili.”
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin cire tallafin man fetur da kuma matsin tattalin arziƙin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Haka kuma, wasu masu ruwa da tsaki a arewacin Najeriya na ci gaba da neman gwamnatin tarayya ta ƙara bayyana ayyukan da take aiwatarwa a Kano da sauran jihohin yankin.




