Majalisar Tarayya ta dage komawar zaman majalisa zuwa 29 ga Satumba
Daga Wakiliya
Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ta dage ranar da sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai za su koma cikakken zaman majalisa daga ranar 15 zuwa 29 ga Satumba 2026.
Magatakardar Majalisar Dokokin Tarayya, Kamoru Ogunlana, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Wakiliya ta ruwaito daga Jaridar The Nation cewa an dauki matakin ne bisa umarnin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
A cewar sanarwar, dagewar ta samo asali ne daga bukatar kammala ayyukan gyare-gyare da ake gudanarwa a zaurukan Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai.
Majalisar ta ce sabon ranar da aka sanya domin komawar ’yan majalisar ita ce Talata, 29 ga Satumba, 2026.
Magatakardar ya bukaci sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da su lura da sauyin ranar, tare da tsara ayyukansu na majalisa bisa sabon jadawalin.




