Tudun Biri kan masu maulidi, Sokoto da kuma Zurmi a Zamfara – A lokacin Christopher Musa an kai hare-hare da dama ta sama kan fararen hula Musulmi wanda aka ce anyi ne bisa kuskure… kuma babu wanda ya zargi Christopher Musa da yunƙurin kawar da Musulmi…
Wai Hana Kashe Mutane A Gwanin Gora Lokacin El-Rufai Shine Raba Kaduna?
Daga Wakiliya
A lokacin da Christopher Gwabin Musa yake rike da mukamin Babban Hafsan Tsaron Najeriya, an samu hare-haren sama da dama da suka shafi fararen hula Musulmi, inda aka bayyana cewa an yi kuskure wajen kai hare-haren.
Misali, a ranar 3 ga Disamba, 2023, harin Tudun Biri a Kaduna ya kashe Musulmi da dama da ke bikin Maulidi. Haka kuma, a ranar 25 ga Disamba, 2023, wani hari a Sokoto ya kashe wasu fararen hula Musulmi da ke barci. A ranar 13 ga Janairu, 2025, kuma wani hari a Zurmi, Zamfara, ya sake salwantar da rayukan fararen hula da dai sauran su.
Duk da wadannan abubuwan da suka faru a lokacin da yake rike da mukaminsa, ba a zarge shi da cewa yana da wani shiri na kawar da Musulmi ba.
Yanzu kuma, Ministan Tsaron yana zargin tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da hannu wajen abubuwan da suka faru a Kudancin Kaduna.
Tambayar da ya kamata a yi ita ce: Shin irin wannan zargi ya dace a yi shi ba tare da gabatar da kwararan hujjoji ba? Ko kuma ana iya cewa shima da gangan ya shirya kashe Musulmai a waɗannan hare-haren da aka ce anyi bisa kuskure?
Idan mutum yana zargin wani da shirya kisan fararen hula, ya kamata ya fito da hujjoji bayyanannu, ba kawai zargi da kalaman siyasa ba.
Haka kuma, bai kamata a yi amfani da irin wadannan zarge-zarge wajen kara rura rikicin addini ko kabilanci a Kaduna ba. Rayukan mutane ne abin magana, kuma kowa ya cancanci adalci.
Shin ko dai hana tare mutane a Gwanin Gora da sauransu ana kashe su shine raba Kaduna da Musa ke nufi?
A siyasa, ana iya sukar mutum, amma ya kamata a bambanta tsakanin zargin siyasa da gaskiyar da aka tabbatar da ita.
Saboda haka, maimakon musayar zarge-zarge, abin da ya fi dacewa shi ne a fito da hujjoji, a binciki duk wani kisan fararen hula, sannan a tabbatar da cewa wadanda suka yi laifi sun fuskanci hukunci – ba tare da la’akari da addininsu ko matsayinsu na siyasa ba.
Wakiliya ~ Muhammad Ƙona




