Gaskiya Ko Siyasa? Tambayar Da Ya Kamata Ministan Tsaro Ya Amsa – Me El-Rufai Ya Hana Sojoji Yi A Kudancin Kaduna?

DA DUMI-DUMI

Gaskiya Ko Siyasa? Tambayar Da Ya Kamata Ministan Tsaro Ya Amsa – Me El-Rufai Ya Hana Sojoji Yi A Kudancin Kaduna?

Daga Wakiliya

Shin kun san cewa Christopher Musa ne kaɗai daga cikin waɗanda Nasir El-Rufai ya nemi alfarmar a ba wa muƙami a Sojoji, bayan Tinubu ya ci zaɓen 2023, saboda burin a ƙara yaƙi da rashin tsaro musamman a Kudancin Kaduna?

El-Rufai ya nemi a naɗa Musa Shugaban Sojin Kasa, Chief of Army Staff (COAS), amma daga baya Tinubu ya naɗa shi Shugaban Hafsoshin Tsaro, Chief of Defence Staff (CDS).

Saboda haka, abin mamaki ne yau a ji jigon APC, Ministan Tsaro Honourable Christopher Musa yana zargin El-Rufai da hannu wajen matsalolin tsaro a Kudancin Kaduna.

Musa ba ɗan kallo ba ne a lokacin mulkin El-Rufai. Ya kasance babban jami’in soja, kuma ya riƙe muhimman mukamai a rundunar soji. Don haka tambayar ita ce: A lokacin, me Musa ya ba El-Rufai shawara kan yadda za a kawo ƙarshen rashin tsaro, wanda El-Rufai ya ƙi aiwatarwa?

Idan da gaske El-Rufai ne ke da alhakin rashin tsaron, me ya sa ba a fito an fallasa abin da ya yi na hana sojoji yin aikin da ya dace su yi ba?

Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, a lokacin da ake ta zargin wani Sanata da hannu wajen ɗaukar nauyin ɗan ta’adda Dogo Gide, wanda ya addabi wasu al’ummomin Kudancin Kaduna, maimakon Musa yi magana kan wannan batu, sai ya koma kan El-Rufai da zarge-zargen da basu da tushe mararsa amfani.

El-Rufai a yanzu haka yana fuskantar bincike kan zargin almundahana, amma inda gaskiya ne, me yasa a tsawon lokacin su Musa suka kasa samun hujjar da za su laƙa da zai tabbatar don a tuhume shi da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci?

A matsayinka na Ministan Tsaro, Christopher Musa ya kamata ya mayar da hankali kan kawo ƙarshen rashin tsaro, ba amfani da batun tsaro wajen kai wa tsohon gwamna hari na siyasa ba.

Idan akwai hujja kan El-Rufai, a gabatar da ita. Idan babu, ya kamata a daina amfani da rashin tsaron Kudancin Kaduna a matsayin makamin siyasa.

Yanzu dai Honourable Christopher ne jagoran tsaro a Najeriya, tambayar ita ce, shin me ya yi kuma ya sauya?

Ra’ayin Imran Usman Wakili

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img