Kiran ‘Yan Bindiga ‘Yan Ta’adda kuskure ne shi ya rufe kofar yin sulhu da su -Gumi

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya soki matakin Gwamnatin Tarayya na ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, yana mai cewa hakan na iya ƙara tsananta matsalar tsaro tare da rufe hanyoyin tattaunawa da su.

A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, Gumi ya ce wasu daga cikin ƙungiyoyin ‘yan bindiga sun nuna a baya cewa a shirye suke su yi sulhu, don haka bai kamata a yi gaggawar sanya musu lakabin ‘yan ta’adda ba.

Ya bayyana cewa a wasu lokuta, wasu ‘yan bindiga sun taimaka wajen kama mambobin Boko Haram tare da miƙa su ga jami’an tsaro a Jihar Zamfara.

Malamin ya ƙara da cewa ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ya sanya malamai da masu shiga tsakani rasa damar tattaunawa da su domin neman mafita ta zaman lafiya.

Kalaman na Gumi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan hanyoyin da suka dace wajen kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga da rashin tsaro a Najeriya.

#Wakiliya |

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img