Ana yi wa wani malamin jami’a a Kano jina-jina kan zargin neman lalata da ɗalibarsa matar aure

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Wani malamin jami’a da ke koyarwa a wasu manyan jami’o’i a Kano ya shiga cece-kuce bayan wasu bidiyo da rahotanni suka bazu a kafafen sada zumunta, inda ake zargin an yi masa duka sakamakon wata takaddama da ta shafi ɗalibarsa.

Rahotannin da ke yawo sun ce ana zargin malamin ya shafe kusan shekara biyu yana ƙin amincewa da aikin binciken kammala karatun (project) na wata ɗaliba, tare da zargin cewa ya nemi ta amince da yin lalata da shi kafin ya sahale mata aikin.

A cewar waɗanda suka wallafa rahotannin, ɗalibar ta sanar da mijinta abin da take zargin yana faruwa, inda ake zargin suka shirya ganawa da malamin domin suyi lalatar. Rahotannin sun ce lokacin da malamin ya isa wurin da aka tsara ganawar domin yin lalatar ne aka yi masa duka.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Wakiliya ba ta sami damar tabbatar da sahihancin zarge-zargen da ke yawo ba.

Haka kuma, babu wata sanarwa daga jami’o’in da ake danganta malamin da su ko kuma daga hukumomin tsaro da ke tabbatar da faruwar lamarin. Kazalika, ba a ji ta bakin mutumin da ake yi wa zargin ba amma dai bidiyoyin sun bazu na yadda ake dukansa.

Wakiliya na ci gaba da bibiyar lamarin, kuma za ta kawo muku ƙarin bayani idan an samu sahihan bayanai daga ɓangarorin da abin ya shafa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img