Za a kafa sabbin sansanin sojoji a kananan hukumomin dake fuskantar barazana a Kano

DA DUMI-DUMI

Za a kafa sabbin sansanonin sojoji a kananan hukumomin dake fuskantar barazana a Kano

Daga Wakiliya

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta kafa ƙarin sansanonin sojoji a wasu ƙananan hukumomin jihar da ke fuskantar barazanar tsaro.

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta na jihar, Mohammed Taju Usman, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Talata.

Ya ce an sake tabbatar da wannan mataki ne yayin wani taro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi da shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

A cewarsa, an tattauna kuma an amince da shirin ne tsakanin gwamnan da Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya).

Kwamishinan ya ce kafa sansanonin zai ƙara ƙarfafa tsarin tsaron da ake da shi a ƙananan hukumomin da abin ya shafa.

Ya ce manufar shirin ita ce ƙarfafa tsaro, sauƙaƙa kai ɗaukin gaggawa yayin fuskantar barazana, da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wasu daga cikin ƙananan hukumomin da ke kan iyakokin jihar Kano da aka sha samun rahotannin satar mutane, ‘yan bindiga da satar shanu sun haɗa da Shanono, Bagwai da Tsanyawa.

 

Fitilun kan titi masu amfani da hasken rana

A wani ɓangare kuma, kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da sanya fitilun kan tituna masu amfani da hasken rana a kowace daga cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Ya ce matakin zai taimaka wajen samar da haske a wuraren taruwar jama’a, ƙara tsaro da kuma tallafa wa ci gaba mai ɗorewa.

Kazalika, ya ce gwamnatin jihar na shirin samar da wuraren cajin motocin lantarki a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano.

Ya bayyana cewa aikin zai fara ne a matsayin gwaji, sannan ana sa ran za a faɗaɗa shi zuwa wasu wurare idan aka samu nasara.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

An kashe mutumin da ake zargi ya daba wa limamin Juma’a a Wuka a Sokoto

Rahotanni sun ce matashin, wanda aka bayyana da suna Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci sallar, kuma ya kai wa malamin hari har sau biyu.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img