Za A Fara Baiwa Motocin Masu Nakasa Lambobin Mota Na Musamman A Lagos

DA DUMI-DUMI

Gwamnatin Jihar Legas ta sanar da shirinta na ƙaddamar da lambobin mota na musamman ga masu nakasa domin sauƙaƙa tantance su da inganta zirga-zirgarsu a faɗin jihar.

Shirin ya samo asali ne daga haɗin gwiwar Hukumar Kula da Harkokin Masu Nakasa ta Jihar Legas (LASODA) da Hukumar Kula da Rajistar Motoci ta Jihar Legas (MVAA), inda suka tattauna hanyoyin aiwatar da tsarin.

Sakataren dindindin na MVAA, Abdulrasheed Muri-Okunola, ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufar Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta gina Legas mai bai wa kowa dama ba tare da ware kowa ba.

A cewarsa, lambobin motocin na musamman za su taimaka wajen sauƙaƙa gano masu nakasa, ƙara musu damar samun sauƙin zirga-zirga, tare da inganta tsarin sufuri mai haɗa kowa da kowa.

Muri-Okunola ya bayyana cewa tuni aka fara tattaunawa da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) kan yadda za a aiwatar da shirin, yana mai tabbatar da cewa za a fara matakan gudanarwa domin ganin ya zama gaskiya.

A nata ɓangaren, Babbar Manajar LASODA, Adenike Oyetunde-Lawal, ta ce shirin zai shafi dukkan rukunin masu nakasa, har da iyaye da masu kula da yara masu nakasa.

Ta bayyana cewa tsarin zai inganta tantance masu nakasa, ƙara musu damar samun tallafi da sauƙaƙa musu amfani da ayyukan gwamnati, tare da jaddada cewa gina al’umma mai haɗa kowa da kowa nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane ɓangare.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img