Ba Zan Mika Wuya ga Masu Neman Kayar da Ni a 2027 Ba, Za Mu Gwabza Har Zuwa Faɗan Ƙarshe — Tinubu

DA DUMI-DUMI

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai mika wuya ga masu neman karɓe masa mulki a zaɓen 2027 ba, yana mai cewa siyasa gasa ce, kuma zai fafata da su har zuwa ƙarshe.

 

Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Talata yayin da ya karɓi baƙuncin Kungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (Catholic Bishops Conference of Nigeria) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

 

Ya ce duk wanda ke son kayar da shi yana da ‘yancin yin hakan, amma ba zai ba su damar samun nasara cikin sauƙi ba.

 

“Duk wanda yake son karɓe min mulki zai yi ƙoƙari. Amma ba zan shimfiɗa musu tabarma ba. Za mu gwabza har zuwa layin ƙarshe. Hakan ne adalcin siyasa,” in ji Tinubu.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img