Tinubu Na Aiki Daga Safe Har Dare, Har Yanzu Yana Da Ƙwarinsa — Shugaban APC, Yilwatda

DA DUMI-DUMI

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yi watsi da ikirarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaji da jagorantar Najeriya.

Yilwatda ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a tashar Channels Television, inda ya ce Shugaba Tinubu na gudanar da ayyukansa tun daga safe har zuwa dare, kuma har yanzu yana da ƙwarin guiwar ci gaba da cika alkawuran da ya ɗauka ga ‘yan Najeriya.

Ya ce, “Ina so in tambayi Peter Obi, shin shugaban ƙasa zai shiga wasan dambe ne ko gudun mita 400? Ta yaya za a ce mutumin da ke aiki daga safe har dare ya gaji?”

Shugaban APC ya kuma ce miliyoyin ɗalibai da iyaye mata da ke cin gajiyar shirin NELFUND ba za su yi fatan Shugaba Tinubu ya sauka daga mulki ba.

A cewarsa, ayyukan manyan tituna da tashoshin jiragen ruwa da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, ciki har da titin Lagos zuwa Calabar, da sabbin tashoshin jiragen ruwa a Calabar, Akwa Ibom, Fatakwal, Ondo da Legas, sun nuna cewa gwamnatin na ci gaba da mayar da hankali kan bunƙasa ƙasa.

Yilwatda ya kuma ce ayyukan gyaran filayen jiragen sama da ake yi a sassan ƙasar nan, ciki har da Arewa, shaida ce cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img