Yara 3 cikin 4 a Najeriya ba sa iya karatu kafin su kai shekara 10 -inji Ministan Ilimi

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa yara uku cikin huɗu a Najeriya ba sa iya karantawa tare da fahimtar rubutun da ya dace da shekarunsu kafin su kai shekara 10, lamarin da ta ce na nuna matsalar ilimi mai tsanani a ƙasar.

Ministan Ilimi, Olatunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taro kan inganta sakamakon koyo ta hanyar amfani da fasahar zamani.

A cewarsa, Najeriya ba ta da wani zaɓi illa ta rungumi koyarwa ta hanyar fasahar zamani domin magance matsalar, yana mai cewa ci gaba da dogaro da tsohuwar hanyar koyarwa kaɗai ba zai wadatar ba.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta samar da dandamalin koyon ilimi na zamani kamar Nigeria Learning Passport da wasu, amma amfani da su har yanzu bai kai yadda ake buƙata ba.

Ministan ya bayyana cewa duk da samun masu amfani kusan miliyan 2.3 a Nigeria Learning Passport, adadin ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da kimanin ɗalibai miliyan 67 da ke makarantun firamare da sakandare a faɗin Najeriya.

Ya buƙaci gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi su ƙara amfani da waɗannan dandamali domin inganta koyarwa da rage ƙarancin ƙwararrun malamai, musamman a darussan Lissafi, Turanci, Kimiyyar Jiki da Kimiyyar Sinadarai.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img