Atiku Ya Zaɓi Amaechi A Matsayin Mataimakin Takararsa Ta Shugaban Ƙasa

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zaɓi tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakin takararsa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce ta riga ta miƙa sunaye da bayanan Atiku da Amaechi cikin nasara zuwa shafin karɓar sunayen ‘yan takara na Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya sanar da hakan a shafinsa na X, inda ya ce matakin na nuna yadda ADC ke ci gaba da shirye-shiryenta domin babban zaɓen 2027.

A cewarsa, jam’iyyar na da burin bai wa ‘yan Najeriya wata madadin gwamnati da ta ginu kan ƙwarewa, haɗin kai da kuma sabunta ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img