Daga Wakiliya
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) sun tattara jimillar Naira biliyan 203.61 a watan Afrilu 2026, daga cikin Naira biliyan 252.43 da suka caji kwastomomi.
A cewar hukumar, hakan na nufin an karɓo kusan kashi 80.66% na kuɗin da aka caji, yayin da adadin kuɗin da aka tattara ya ƙaru da kashi 3.81% idan aka kwatanta da watan Maris.
Sai dai NERC ta ce akwai babban bambanci tsakanin kamfanonin, inda Kano DisCo, Kaduna DisCo da Jos DisCo suka kasance mafi raunin aiki a fannin tara kuɗaɗen wutar lantarki.
Rahoton ya nuna cewa Kano DisCo ce ta zo ƙarshe, inda ta samu ƙimar tara kuɗi (recovery efficiency) ta kashi 43.15% kacal. Kamfanin ya tattara Naira biliyan 8 ne daga cikin Naira biliyan 16.04 da ya caji kwastomomi.
Haka kuma, Kaduna DisCo ta tara Naira biliyan 5.83 daga cikin Naira biliyan 10.52, yayin da Jos DisCo ta tattara Naira biliyan 6.51 daga cikin Naira biliyan 11.05 da ta caji.
A gefe guda kuma, Eko DisCo ce ta kasance mafi kyawun kamfani, inda ta zarce ƙimar kuɗin da aka amince ta tara, tare da samun 102.09% recovery efficiency. Port Harcourt DisCo da Abuja DisCo su ma sun kasance cikin mafi kyawun masu gudanar da aiki.
NERC ta ƙara da cewa duk da ƙarin kuɗin da aka tattara a watan Afrilu, har yanzu akwai babban gibi tsakanin kuɗin da ya kamata a karɓa da kuma abin da aka samu, lamarin da ke ci gaba da kawo cikas ga saka hannun jari da inganta harkar rarraba wutar lantarki a Najeriya.





