Bayan Bincike: An gano alamun man fetur da iskar gas da ma’adanan samar da lantarki a Plateau

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Wani bincike da ya shafe shekaru biyar, wanda Petroleum Technology Development Fund (PTDF) ya gudanar tare da Jami’ar Jos, ya gano alamun da ke nuna akwai yiwuwar samun man fetur da iskar gas a wasu sassan Jihar Plateau.

A wajen gabatar da sakamakon binciken a Jami’ar Jos, Farfesa Nuhu Kadai Samaila ya ce binciken ya tabbatar da cewa yankin Shendam na da siffofin kasa da ke nuna yiwuwar samar da sinadaran man fetur.

Ya bayyana cewa abin da binciken ya fi tabbatarwa a halin yanzu shi ne akwai yiwuwar iskar gas, yayin da kuma aka samu wasu alamun da ke nuna yiwuwar samun danyen mai, musamman a yankunan Langtang ta Arewa da Langtang ta Kudu.

A cewarsa, ana bukatar a gudanar da binciken seismic survey tare da haɗin gwiwar NNPCL domin tantance yawan albarkatun da kuma ko za su iya zama abin hakowa ta kasuwanci.

Baya ga man fetur da iskar gas, binciken ya kuma gano ma’adinan barite da kuma wasu albarkatun makamashin zafi daga karkashin kasa (hydrothermal energy) da za su iya taimakawa wajen samar da wutar lantarki.

Shugaban PTDF, Farfesa Shuaibu Shehu Aliyu, ya bukaci jami’o’in Najeriya su mayar da hankali kan binciken da zai kai ga samar da hanyoyin jawo zuba jari da ci gaban masana’antu, yayin da Shugaban Jami’ar Jos, Farfesa Tanko Ishaya, ya ce binciken ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i da masana’antu wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Rahoton ya ce sakamakon wannan bincike zai taimaka wajen jagorantar ƙarin bincike da yanke shawara kan yiwuwar hako man fetur da iskar gas a Plateau da sauran yankunan Benue Trough.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img