Wani Sufeton Dan sandan a Sokoto ya fadi ya mutu jim kadan da atisayen motsa jiki

DA DUMI-DUMI

Wani Sufeton Dan sandan a Sokoto ya fadi ya mutu jim kadan da atisayen motsa jiki

Daga Wakiliya

Wani sufeto na rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ya mutu bayan ya fadi jim kadan da kammala atisayen motsa jiki da rundunar ke gudanarwa duk mako.

Marigayin, Sufeto Adamu Isah, yana aiki ne a sashen ayyuka na rundunar ’yan sandan jihar.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar ranar Alhamis, Isah ya fadi ne bayan ya dawo daga atisayen Walkathon da aka gudanar a hedikwatar rundunar ranar Laraba.

Sanarwar ta ce an garzaya da shi asibiti domin samun kulawar gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img