Kamfanin Amurka dake binciken zargin fataucin miyagun ƙwayoyin Tinubu ya ce an yi masa tayin cin hancin Dala miliyan $3m don ya daina bibiyar lamarin
Daga Wakiliya
Wani kamfanin ba da shawarwari kan harkokin siyasa da lobbi da ke Amurka, Von Batten-Montague-York, ya ce ya kai wa Ma’aikatar Shari’a ta Amurka (DOJ) rahoton wani tayin cin hancin dala miliyan uku ($3m), Kimanin Naira Biliyan 4bn.
Kamfanin ya ce an yi tayin ne domin dakatar da binciken da ake zargin yana da alaƙa da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan zargin fataucin miyagun ƙwayoyi.
A wani saƙo da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, ya ce shugaban kamfanin, Dr Von Batten, ya ƙi amincewa da tayin, tare da adana kwafin saƙonnin da aka aika masa.
Kamfanin ya ce saboda girman kuɗin da aka ambata, da kuma shawarar gudanar da wata ganawa ta sirri a Landan, tare da amfani da saƙonnin (view once) da ke ɓacewa, ya ga ya dace ya kai lamarin ga hukumomin Amurka.
Ya ce ya kuma miƙa hotunan (screenshots) na saƙonnin da aka tura masa ga ma’aikatar Shara’a ta Amurka, DOJ.
Kamfanin ya ƙara da cewa yanzu zai bar Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta tantance ko saƙonnin sun isa a buɗe wani ƙarin bincike.
Sai dai zuwa yanzu ba a bayyana wanda ya yi tayin kuɗin ko kuma ko DOJ ta fara wani bincike a hukumance kan lamarin ba.




