Jihohin Najeriya Hudu Sun Zuba Sama da Naira Biliyan 500 a Kamfanonin Jiragen Sama

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Aƙalla gwamnatocin jihohi huɗu a Najeriya sun kashe sama da Naira biliyan 500 wajen kafa kamfanonin jiragen sama da sayen jirage a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Jihohin da suka mallaki kamfanonin jiragen sama sun haɗa da Akwa Ibom (Ibom Air), Cross River (Cally Air), Enugu (Enugu Air) da Bayelsa (Pioneer Air), yayin da Ogun, Anambra da Lagos ke shirin kafa nasu.

Masana harkar sufurin jiragen sama sun nuna damuwa kan yadda jihohi ke zuba makudan kuɗaɗe a wannan fanni duk da matsalolin ababen more rayuwa, lafiya da ilimi da ke bukatar kulawa.

Duk da haka, wasu masana sun ce kamfanonin jiragen sama na iya taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma haɗa sabbin hanyoyin zirga-zirga.

Ibom Air ta bayyana cewa ta samu kudin shiga na Naira biliyan 96 tare da ribar aiki ta Naira biliyan 16.6 a shekarar 2025, abin da ya sa ake kallonta a matsayin mafi nasara cikin kamfanonin jiragen saman da jihohi suka kafa.

Sai dai masana sun yi gargadin cewa kasuwar sufurin jiragen sama ta Najeriya na iya kasa ɗaukar yawan kamfanonin da ake ƙara kafawa, musamman idan ba a tabbatar da dorewa, gaskiya da ingantaccen tsarin gudanarwa ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img