Shugaban DSS ya hana Jami’an DSS kama mutane kan rikicin farar hula
Daga Wakiliya
Daraktan-Janar na Hukumar DSS, Oluwatosin Ajayi, ya ce ya umarci jami’an hukumar da su daina kama mutane saboda batutuwan da suka shafi rikicin farar hula.
Ajayi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai da aka wallafa ranar Alhamis.
Ya ce matakin na daga cikin sauye-sauyen da yake yi domin tabbatar da bin doka da mutunta haƙƙin bil’adama.
“Na gaya wa jami’aina cewa kada a kama kowa kan wani lamari na farar hula,” in ji shi.
Ya ce hukumar ta fara bambance tsakanin rikicin farar hula da manyan laifuka, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da ƙarfi wajen warware rikicin farar hula ba.
Ya kuma bayar da misalan wasu shari’o’i da suka shafi Pat Utomi, SERAP da Omoyele Sowore, inda ya ce DSS ta koma kotu maimakon kama waɗanda abin ya shafa.
Ajayi ya ce har a batutuwan da suka shafi ’yan jarida, hukumar za ta fi son bin hanyar kotu wajen warware matsaloli.




