El-Rufai ya aikata munanan abubuwa a Kaduna — ‘Ba za mu taba farin ciki da shi ba’ — Janar Musa

DA DUMI-DUMI

El-Rufai ya aikata munanan abubuwa a Kaduna – ‘Ba za mu taba farin ciki da shi ba’ — Janar Musa

Daga Wakiliya

Ministan Tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce gwamnatin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ta janyo rabuwar kan al’ummar jihar.

Janar Musa ya ce lokacin da El-Rufai ke mulki, yanayin siyasa da zamantakewa a Kaduna ya kasance mai cike da tashin hankali.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da shirin Channels Television One-on-One.

A cewarsa, El-Rufai ya aikata abubuwa da dama da suka cutar da jihar, yana mai cewa tsohon gwamnan ya “raba Kaduna gida biyu ”.

Ya kuma yaba wa gwamnan Kaduna na yanzu, Uba Sani, bisa abin da ya ce ya yi wajen kawo karshen wannan rarrabuwar.

“Ba za mu taba farin ciki da mutumin da ya tsara tare da kashe mutanenmu da gangan ba,” in ji Janar Christopher Musa.

Sai dai ministan bai yi karin bayani kan takamaiman shirin da ya ce El-Rufai ya yi na kashe mutanen ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img