Wa Ya Fada Miki Cewa Bai Son Matarsa Ta Farko? – Waraka Temple Ta Gargaɗi Mata Masu Shirin Zama Mata Na Biyu

Daga Wakiliya

“Wa Ya Ce Mijinki Bai Son Matarsa Ta Farko Ba?” – Waraka Temple Ta Gargaɗi Mata Masu Shirin Zama Matan Aure Na Biyu

Mashahuriyar mai ba da shawara kan zamantakewar aure da iyali, Waraka Temple, ta yi gargaɗi ga mata masu shirin zama mata na biyu da kada su shiga gidan miji da girman kai ko tunanin cewa mijin ya daina son matarsa ta farko.

Da take magana a wata tattaunawa da aka yi da ita a shirin Fact News Hausa Podcast, Waraka Temple ta ce wasu sabbin amaren kan shiga gidan aure da tunanin cewa kasancewar namiji ya aure su na nufin ya watsar da matarsa ta farko, alhali hakan ba gaskiya ba ne.

“Wa ya gaya miki cewa bai son matarsa ta farko? Maza dai sun iya nuna abubuwa ta wata hanya,” in ji ta.

Ta ce wasu sabbin mata kan yi ƙoƙarin burge mijinsu fiye da kima ta hanyar ɗaukar nauyin ayyuka masu wahala kamar wanke mota da sauran hidimomi da ba za su iya ci gaba da yi ba, domin kawai su nuna sun fi matar farko.

Waraka Temple ta ƙara da cewa matsayin matar farko ba abu ne mai sauƙin gogewa ba, domin sau da yawa ya samo asali ne daga shekaru na haƙuri, zaman tare da kuma ƙaunar da aka gina a cikin iyali. Saboda haka, ta shawarci mata masu shiga gidan miji a matsayin mata na biyu da su kasance masu tawali’u, nutsuwa da tsoron Allah, maimakon neman gogayya da matar farko.

A nasa bangaren, ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin, A. Ladan Zamani, ya jaddada cewa babban nauyi yana kan miji wajen tabbatar da adalci tsakanin matansa.

Ya ce duk da cewa addini da al’ada sun amince da auren fiye da mace ɗaya, hakan yana tare da sharadin yin adalci da kyakkyawan tafiyar da gida.

“Idan miji ba zai iya yin adalci tsakanin matansa ba, to manufar ƙara aure ta rasa ginshiƙinta,” in ji A. Ladan Zamani.

Tattaunawar ta jawo ce-ce-ku-ce da martani daga al’ummar Hausawa, inda da dama ke ganin ta sake haskaka muhimmancin mutunta juna, hakuri da kuma fahimtar juna a gidajen da ake zaman aure fiye da mace ɗaya.

DA DUMI-DUMI

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Tsoron Talauci Na Jefa Mutane Da Dama Cikin Matsananciyar Damuwa – Masana

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa, Kimanin Naira Tiriliyan 16, Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Aliko Dangote Ya Yi Wasiyyar A Ware Kashi Ɗaya Bisa Uku Na Dukiyarsa Domin Ayyukan Jin Ƙai — Halima Dangote

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, sanye da dankwali da aka rubuta “JESUS”

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rashidat Ajibade, na bayyana bangaskiyarta ga Yesu a duk inda ta je.

Har Tsawon Wane Lokaci Za a Iya Ajiye Kifi a Firiza Kafin Ya Lalace?

Yawan Lokacin da Kifi Zai Iya Ɗauka a Firiza Kafin Ya Lalace

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Wani Magidanci a Kano Ya Kashe Wani Mutum Saboda Ya Yi Zargin Yana Neman Matarsa – Kiyawa

Kanun Labarai

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Shaida Mata Zai Auri Wata – Rundunar Yan Sanda

Budurwa Ta Yanke Gaban Saurayinta a Kano Bayan Ya Sanar da Ita Cewa Zai Auri Wata — Rundunar 'Yan Sanda

Mata Sun Fi Maza Cika Alƙawarin Biyan Bashi – Inji Rahoton Moniepoint

Moniepoint ta ce alkaluman sun nuna cewa, duk da matsalolin da mata ke fuskanta wajen samun rance saboda buƙatar jingina ko rashin tarihin bashi, suna daga cikin rukunin masu kasuwanci da suka fi nuna amana wajen biyan bashin da suka karɓa.

Kana Tsoron Ciwon Suga? Ga Abin da Masana Suka Ce Kan Cin Kankana da Gwanda

Kankana da Gwanda: Wanne Ya Fi Amfani Wajen Rage Haɗarin Kamuwa da Ciwon Suga?
spot_img

Labarai masu alaka

Sauran bangarori

spot_imgspot_img