Fadar Shugaban Ƙasa ta yi magana game da halin da Tinubu ke ciki da yasa bai halarci taron MDD ba

DA DUMI-DUMI

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi magana game da halin da Tinubu ke ciki da yasa bai halarci taron MDD ba

Daga Wakiliya

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na cikin ƙoshin lafiya, tana mai cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa duk da kasancewarsa a wajen Najeriya domin hutun shekara.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya ce Tinubu na yin “hutun aiki”, kuma ba lallai ne sai yana Abuja ba kafin ya gudanar da ayyukansa.

Sai dai rashin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya na UNGA a New York ya jawo tambayoyi daga wasu ‘yan siyasa da masu sharhi.

Fadar shugaban ƙasar ta ce Tinubu ya wakilta Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Najeriya a taron.

Ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya a wannan makon, gabanin bikin cikar ƙasar shekaru 66 da samun ‘yancin kai.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img