Tinubu Zai Jinginar Da Takardun Kaɗarorin Gwamnati Don Karbo Bashin Dala Biliyan 5 daga UAE

DA DUMI-DUMI


Daga Wakiliya


Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta jinginar da takardun bashin gwamnati da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 6.65 domin samun bashin dala biliyan 5 daga babban bankin First Abu Dhabi Bank na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

Bisa tsarin yarjejeniyar, gwamnatin za ta jinginar da takardun bashi da suka zarce adadin kuɗin da take karɓa da kusan kashi 133 cikin 100, yayin da bankin zai samar mata da dalar Amurka.

Masana harkokin kuɗi sun bayyana cewa wannan tsari na bai wa gwamnati damar samun kuɗaɗen waje cikin gaggawa ba tare da sake fitar da sabbin takardun bashin ƙasashen waje ba.

Sai dai, sun yi gargadin cewa idan darajar takardun bashin da aka jinginar ta ragu sakamakon sauyin kasuwa ko faɗuwar darajar naira, Najeriya na iya fuskantar buƙatar ƙara jinginar da wasu kadarori.

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da kamfanin Fitch Ratings sun kuma nuna damuwa cewa irin wannan tsarin lamuni na iya rage bayyana ainihin girman bashin da ƙasa ke bin bashi, lamarin da ka iya ƙara haɗarin kuɗi a nan gaba.

Tuni gwamnatin tarayya ta karɓi kason farko na dala biliyan 1.5 daga cikin wannan bashin, wanda ta ce za ta yi amfani da shi wajen aiwatar da kasafin kuɗin 2026, ayyukan more rayuwa da kuma sake tsara wasu basussuka.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img