DSS ta saki wani Dan Arewa da ta tsare bisa kuskure kan zargin alaƙa da Boko Haram, ta ba shi diyyar Naira miliyan 3m

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta saki wani manomi kuma makiyayi, Nura Idris, bayan wani bincike na cikin gida ya tabbatar da cewa babu wata hujja da ke nuna yana da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram.

Rahotanni sun ce Darakta Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi, ne ya bayar da umarnin a sake shi tare da ba shi diyyar gaggawa ta Naira miliyan uku domin rage masa raɗaɗin abin da ya fuskanta.

An kama Nura ne a watan Yunin 2024 a Suleja, jihar Neja, bisa zargin ta’addanci, kafin daga bisani a miƙa shi ga DSS.

Majiyoyi sun bayyana cewa bayan sake nazarin shari’arsa, jami’an binciken DSS sun gano babu wata hujja da ke tabbatar da zargin da ake masa.

Baya ga diyyar kuɗi, DSS ta yi alƙawarin taimaka masa wajen farfaɗo da harkokin kiwon dabbobi domin ya ci gaba da rayuwarsa.

Rahotanni sun kuma ce hukumar na ba wa waɗanda aka wanke daga irin waɗannan zarge-zarge tallafin jinya, kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma taimakon sake komawa rayuwa.

An ce sakin Nura na daga cikin shirin DSS na sake duba tsofaffin shari’o’in tsare mutane domin tabbatar da cewa ba a ci gaba da tsare marasa laifi ba.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img