Matatar Dangote Ta Zarce Amurka Wajen Fitar da Man Jiragen Sama Zuwa Turai

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Matatar Mai ta Dangote ta sake kafa tarihi bayan ta fitar da kimanin tan dubu 466,000 na man jiragen sama zuwa nahiyar Turai a watan Yuni, wanda darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757.

Rahoton S&P Global Commodity Insights ya nuna cewa yawan man jiragen saman da matatar ta aika Turai ya zarce na Amurka a watan Yuni, lamarin da ya sanya Najeriya ta zama ɗaya daga cikin manyan masu samar da wannan nau’in mai ga kasuwar Turai.

Rahoton ya ce fitar da man jirage daga Najeriya zuwa Turai ya ƙaru daga tan dubu 232,000 a watan Mayu zuwa tan dubu 466,000 a watan Yuni, yayin da wanda Amurka ke fitarwar ya ragu zuwa tan dubu 399,000 a wannan lokaci.

Masana sun bayyana cewa ƙarin samar da mai daga matatun Turai, Amurka da Dangote ya haifar da cikar kasuwa, wanda ya sa farashin man jiragen ya fara sauka bayan tashin da aka samu sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

A cewar hukumar kula da mai ta Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority, matatar Dangote ta fitar da lita biliyan 1.66 na kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen waje a watan Afrilu 2026, ciki har da lita miliyan 615 na man jiragen sama.

Ci gaba da ƙara yawan samar da kayayyaki daga matatar Dangote na ƙara tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin ƙasa mai fitar da man fetur da aka tace zuwa kasuwannin duniya, bayan shekaru masu yawa na dogaro da shigo da irin waɗannan kayayyaki.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img