Oluremi Tinubu Ta Ba da Tallafin Naira Biliyan 2 Domin Farfaɗo da Masaƙar “Akwete” Dake Jihar Abia

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

ABIA – Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta sanar da bayar da tallafin Naira biliyan 2 domin farfaɗo da sana’ar saƙar Akwete, ɗaya daga cikin tsofaffin sana’o’in gargajiyar al’ummar Igbo.

Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne yayin ziyararta ta farko zuwa ƙauyen masu saƙar Akwete da ke Jihar Abia.

Ta jaddada muhimmancin bunƙasa al’adun Igbo ta hanyar amfani da tufafin da ake saƙa da hannu na Akwete, tare da yabawa matan yankin bisa jajircewarsu wajen kare wannan gadon al’adu da suka gada tun shekaru masu yawa.

A yayin taron, masu saƙar Akwete sun kuma karrama Uwargidan Shugaban Ƙasar da sarautar gargajiya ta “Ugo Nwanyi” ta Jihar Abia, domin girmama gudummawar da take bayarwa wajen bunƙasa al’adu da ƙarfafa mata.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img