Sabuwar Dokar ‘Yan Sandan Jihohi Ta Hana Hisbah, Amotekun, da Ebube Kafa Dokoki Ko Rike Makami

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Sabuwar kudirin dokar kafa ‘yan sandan jiha ya tanadi cewa ƙungiyoyin tsaron al’umma da ake da su yanzu, kamar Amotekun, Hisbah da Ebube Agu, ba za su koma ‘yan sandan jiha kai tsaye ba, kuma ba za su riƙa ɗaukar makamai ba sai idan Kundin Tsarin Mulki da dokar Majalisar Tarayya sun ba su izini.

Haka kuma, kudirin ya bai wa ‘Yan Sandan Tarayya damar shiga cikin ayyukan ‘yan sandan jiha na ɗan lokaci idan an samu matsalar tsaro da gwamnatin jihar ta kasa shawo kanta, ko kuma idan gwamna ya nemi taimako.

Sai dai dole ne shugaban ƙasa ya amince da irin wannan mataki, tare da bayyana dalili, yankin da abin zai shafa da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka. Haka kuma, za a sanar da gwamnan jihar da Majalisar Dokoki cikin sa’o’i 48.

Kudirin ya kuma tanadi kafa Hukumar Kula da ‘Yan Sandan Jiha (State Police Service Commission) a kowace jiha, wadda za ta riƙa ɗaukar ma’aikata, inganta su, ladabtar da su, tare da kula da ayyukansu. Sai dai naɗin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jiha zai kasance ne da amincewar Majalisar Kula da ‘Yan Sanda ta Ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img