Bashin da Gwamnatin Tinubu Ta Karɓa Ya Ƙaru da Naira Tiriliyan 17.4 Cikin Shekara Guda -CBN

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa bashin da Gwamnatin Tarayya ke karɓa daga cikin gida ya ƙaru da Naira tiriliyan 17.4 tsakanin watan Mayun 2025 da Mayun 2026.

Sabbin bayanan CBN sun nuna cewa jimillar bashin da gwamnatin ta karɓa ya haura daga Naira tiriliyan 22.99 zuwa Naira tiriliyan 40.38, wanda ke nuna ƙarin kashi 75.6 cikin ɗari cikin shekara guda.

Haka kuma, a cikin wata ɗaya kacal, daga Afrilu zuwa Mayun 2026, bashin ya ƙaru da kusan Naira biliyan 780.

Rahoton ya nuna cewa bankuna sun fi karkata wajen saka kuɗaɗensu a takardun bashin gwamnati, kamar Treasury Bills da Government Bonds, maimakon ba kamfanoni da ‘yan kasuwa rance.

A gefe guda, rancen da kamfanoni da gidaje suka samu ya ƙaru ne kaɗan zuwa Naira tiriliyan 81.04 daga Naira tiriliyan 80.59 a watan Afrilu.

Masana tattalin arziƙi sun yi gargaɗin cewa ci gaba da fifita bai wa gwamnati rance na iya rage damar da kamfanoni da masana’antu ke samu na samun jari, lamarin da zai iya kawo cikas ga bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img