Majalisar Dattijai Ta Amince da Kudirin Kafa ‘Yan Sandan Jihohi a Najeriya -ta baiwa Gwamnoni Ikon Naɗa Kwamishinoni

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da kudirin kafa ‘Yan Sandan Jihohi (State Police) bayan sama da kashi biyu bisa uku na sanatoci suka kada kuri’ar goyon baya.

Kudirin ya bai wa gwamnoni ikon naɗa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jiha, tare da amincewar Majalisar Dokokin jihar. Haka kuma, gwamna na da ikon ba kwamishinan umarnin manufofi kan tsaron jama’a da zaman lafiya.

Sai dai kudirin ya haramta amfani da ‘yan sandan jiha wajen kama ko tsangwamar masu sukar gwamnati ba tare da bin doka ba. Haka kuma, ba za a iya cire Kwamishinan ‘Yan Sandan Jiha daga mukaminsa ba sai bisa ƙa’ida, tare da amincewar Majalisar Dokokin jihar.

Bayan amincewar Majalisar Dattijai, kudirin zai wuce zuwa Majalisar Wakilai. Idan ta amince da shi, za a aika shi zuwa Majalisun Dokokin jihohi 36, inda ake buƙatar aƙalla jihohi 24 su amince kafin ya zama wani ɓangare na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Shaharata a ƙauyukan Gombe ta fi abin da ake gani a kafafen sada zumunta’ – Pantami

Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da koyar da matasa sana’o’in zamani, maimakon dogaro da rabon kuɗi.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img