Daga Mamud Galadanci II
Mansurah Isah tana cikin ‘yan gaba-gaba a masu rawar jikin Triple R a farko.
Daga baya ta fice saboda suna kokarin hanata kullo nata alakokin daga Villa a kan dole ta dawo da komai karkashin Triple R.
Ina tuna yadda ta rika zakewa a farkon nan ne amma yanzu kuna gani ta koma yakar Triple R din.
Gaba daya gamayya ce ta son zuciya da tumasanci. Ba wai ta barsu bane don wani abu sai don suna kokarin rufeta da hanata wasu damammaki.
Da naga video din nan nata na kara tabbatar da shirmen su kansu ‘yan siyasar da suke ganin wai wadannan mutanen ne zasu fadawa Al’umma wanda zasu zaba da dalilin zabar nasu.
Gaba dayansu a yunwace suke. Idonsu ya gama rufewa. In ka dunkule su kuma, ba abunda suke karawa ‘yan siyasar APC din bayan bakin jini dorawa kan wanda suke dashi already.
Kamar Musa Mai Sana’a ne ai, sanda aka kafa gwamnati ba’a bashi komai ba, ya dawo yana ta zage-zage. Ana kiransa aka bashi thamanan kaleelan kuma sai ya kara zaucewa, ya koma gidan jiya har ya fi jiyan ma zaucewa.
Shi kansa Rarara din mene bai fada ba a kan Buharina bashi kariya. Amma lokacinsa yana wucewa ya dawo yana tafkar Buhari din da cewa shi ya lalata kasar.
Kasuwa ce ta son zuciya da mutuwar zuciya.
Duk dan siyasar da yake ganin wadannan mutanen ne zasu tallata shi yana yaudarar kansa.
Sannan duk wanda yake kallon wadannan mutanen a matsayin wadanda zasu yi convincing dinsa ya zabi wani, bai cancanci mallakar katin zabe ba kwata-kwata.





