Remi Tinubu ta buƙaci ’yan Najeriya su rage ɓarnar abinci

DA DUMI-DUMI

Remi Tinubu ta buƙaci ’yan Najeriya su rage ɓarnar abinci

Daga Wakiliya

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta buƙaci ’yan Najeriya su rage ɓarnar abinci tare da rungumar hanyoyin da za su taimaka wajen kare muhalli.

Oluremi Tinubu ta yi wannan kira ne a saƙonta na bikin Ranar Tsabtace Duniya ta 2026, wadda aka gudanar a ranar Lahadi ƙarƙashin taken “Daga faranti masu tsafta zuwa birane masu tsafta.”

Ta ce ya zama wajibi gidaje, ’yan kasuwa da al’umma su riƙa sayen, sarrafa, amfani da kuma adana abinci yadda ya kamata.

Ta kuma yi kira da a riƙa zubar da shara yadda ya dace, tare da ƙara amfani da hanyoyin kare muhalli domin samar da al’ummomi masu tsafta da lafiya.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img