Marafa ya ce zai yi murabus idan bai kawo ƙarshen ’yan bindiga a Zamfara cikin shekaru biyu ba

DA DUMI-DUMI

Marafa ya ce zai yi murabus idan bai kawo ƙarshen ’yan bindiga a Zamfara cikin shekaru biyu ba

Daga Wakiliya

Sanata Kabiru Garba Marafa, ɗan takarar gwamnan Zamfara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya yi alkawarin kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga a jihar cikin wa’adin mulkinsa na farko idan aka zaɓe shi a 2027.

Marafa ya ce zai ɗauki matakan da suka dace wajen tunkarar maboyar ’yan bindiga da magance matsalar rashin tsaro a jihar.

“Ko dai in kawo ƙarshen rashin tsaro cikin shekaru biyu, ko kuma in bar ofishin,” in ji Marafa.

Ya ce yana da masaniya kan matsalolin Zamfara saboda kasancewarsa tsohon kwamishina da kuma sanata, yana mai cewa zai ba da fifiko ga tsaro, mata da matasa idan aka zaɓe shi.

Marafa ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ba shi da sauran ’yan takarar ADC goyon baya a zaɓen 2027.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img