Kashi 80% Na Masu POS A Najeriya Ba Su Da Rajista -inji EFCC

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa binciken da ta fara kan kamfanoni 200 da Hukumar Rijistar Kamfanoni (CAC) ta tura mata ya fara haifar da muhimman sakamako.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gudanarwar CAC ƙarƙashin jagorancin Sanata Ibrahim M. Ida a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Shugaban CAC ya ce abin damuwa ne yadda kusan kashi 20% kacal na masu gudanar da harkar POS suka yi rajista da hukumar, lamarin da ya saɓa da dokokin CAMA 2020 da kuma ƙa’idodin Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ya kuma yi gargaɗin cewa ana amfani da wasu POS marasa rajista wajen karɓa da tura kuɗaɗen ayyukan laifi, ciki har da kuɗin fansar masu garkuwa da mutane.

A nasa ɓangaren, shugaban EFCC ya ce sama da kashi 80% na laifukan kuɗi a Najeriya na da alaƙa da damfara a harkokin kwangila da kuma wasu kamfanoni masu rajista. Ya ƙara da cewa akwai buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin EFCC da CAC domin dakile laifukan kuɗi tare da kare tsarin kuɗaɗen ƙasar.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img