Daga Wakiliya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci na Legas, Sheikh Tijani Gbajabiamila, inda ya bayyana cewa ya daɗe yana cin moriyar ilimi da shawarwarin marigayin tun kafin ya zama Gwamnan Jihar Legas.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa da ya fitar ranar Talata, Tinubu ya ce Sheikh Tijani Gbajabiamila ya kasance malami mai zurfin ilimin Alƙur’ani da addinin Musulunci, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen wa’azi, tarbiyya da hidimar al’umma.
Shugaban ƙasar ya ce lokacin da yake Gwamnan Legas, da ma tun kafin wannan lokaci, marigayin ya kasance yana ba shi jagoranci da shawarwari kan harkokin addini da rayuwa.
Tinubu ya yabawa gudummawar da Sheikh Tijani Gbajabiamila ya bayar wajen bunƙasa ilimin Musulunci, tarbiyyar matasa, sasanta rikice-rikice da kuma inganta fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai.
Ya ce marigayin ya kasance mutum mai haɗa kan al’umma, wanda hikimarsa da iliminsa suka sa ya zama abin girmamawa a cikin gida da wajen Najeriya.
Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Tijani Gbajabiamila, Gwamnatin Jihar Legas, almajiransa da daukacin masu alhini, yana mai cewa gadon alheri da malamin ya bari zai ci gaba da amfani ga al’umma.





