NESREA Ta Gargadi Jama’a Kan Kusantar Wata Farar Kumfa da Ta Bayyana a Hanyar Kaduna – Abuja, Ta Ce Ana Zargin Guba Ce Mai Hatsari

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Kasa (NESREA) ta fara bincike kan wani zargin zubar da sinadari mai hatsari a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan da aka ga wani farin kumfa ya mamaye wurin.

Tawagar NESREA ta ofishin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Kodinetan jihar, Hena Dangari Emmanuel, ta kai ziyara wurin domin gudanar da bincike tare da ganawa da Kwamandan ‘Yan Sanda na Jere, ACP Sani Zubairu, Kwamandan Hukumar FRSC na yankin da kuma shugaban al’umma.

Binciken farko ya nuna cewa wani babban motar dakon kaya ya yi hatsari, lamarin da ya haddasa zubar da abin da yake dauke da shi a wurin.

Hukumar ta ce ta tattara bayanai daga jami’an tsaro da mazauna yankin, sannan ta kwashe samfurin farin kumfar, kasa da kuma ruwan wani rafin da ke kusa domin gudanar da gwajin dakin bincike.

NESREA ta gargadi jama’a da su guji taba farin kumfar, ruwan rafin da kuma kasar da ke kewaye da wurin har sai an kammala bincike, domin kauce wa yiwuwar haduwa da sinadarai masu hadari.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img