Ko Maƙiyina Zai Shaida Cewa Kano Tawa Ce – Kwankwaso Ya Yi Martani Ga Ali Modu Sheriff

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya


Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da kalaman tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, wanda ya ce haɗakarsa da Peter Obi ba za ta samu karɓuwa a Kano da sauran Arewacin Najeriya ba.

Kwankwaso ya bayyana a wata hira da tashar Channels TV cewa ƙarfin siyasarsa a Kano abu ne da kowa ya sani, har ma da abokan hamayyarsa.

Ya ce Ali Modu Sheriff ya faɗi hakan ne kawai domin ya nuna wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa yana yi masa aiki.

> “Ko maƙiyina mafi tsanani zai gaya maka cewa Kwankwaso yana da Kano. Ba na daga cikin ‘yan siyasar da ke yawan taƙama. A maimakon haka, ina farin ciki idan mutane suka raina ƙarfinmu, saboda hakan yana sa su yi sakaci yayin da muke ci gaba da aiki,” in ji Kwankwaso.



Tsohon gwamnan Kano ya kuma bayyana cewa haɗin gwiwar Kwankwasiyya da magoya bayan Peter Obi (Obidients) zai kawo manyan sauye-sauye a siyasar Najeriya kafin zaɓen 2027.

Kwankwaso ya ƙara da cewa Peter Obi ba sabon ɗan takara ba ne a Arewacin Najeriya, yana mai tunatar da cewa ya samu sama da ƙuri’u miliyan biyu a yankin a zaɓen da ya gabata.

A cewarsa, haɗakar magoya bayan Obi da Kwankwasiyya za ta ba da mamaki musamman daga matasa, waɗanda ya ce ba sa damuwa da siyasar rarrabuwar kawuna da wasu ke ƙoƙarin yadawa.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img