Ku ƙara ba mu dama mu kammala abunda da muka fara – Tinubu
Daga Wakiliya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi ’yan Najeriya su ƙara ba gwamnatinsa lokaci domin ta kammala sauye-sauyen da ta fara.
Tinubu ya bayyana hakan ne a saƙon da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya isar a madadinsa yayin sallar Juma’a ta musamman a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce gwamnati na gyara kura-kurai da damar da gwamnatocin baya suka rasa, yana mai kira ga ’yan Najeriya da kada su yanke ƙauna.
Shugaban ya ce Najeriya na kan hanyar samun ci gaba, kuma zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki za su dawo yayin da ake ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen gwamnati.
Ya ƙara da cewa ya kamata ’yan Najeriya su ƙara bai wa gwamnatinsa dama domin ta kammala ayyukan da ta fara.




