Nan da 2036 Kuɗi Ba Za Su Ƙara Tasiri ba, AI Za Ta Sauya Tattalin Arziki – Elon Musk

DA DUMI-DUMI

Daga Wakiliya

Shugaban kamfanonin Tesla da SpaceX, Elon Musk, ya bayyana cewa nan da shekarar 2036, kuɗi ba za su ƙara zama abu mai muhimmanci ba yayin da fasahar AI (Basirar Wucin Gadi) da mutum-mutumin aiki (robots) za su iya gudanar da kusan dukkan ayyukan da mutane ke yi.

A wata hira da ya yi da babbar Editar mujallar The Economist, Zanny Minton Beddoes, a masana’antar Gigafactory da ke jihar Texas, Musk ya ce ci gaban AI zai sauya tsarin tattalin arziki gaba ɗaya, inda ya yi hasashen cewa duniya za ta fuskanci raguwar farashi (deflation) maimakon hauhawar farashi (inflation).

Elon Musk ya kuma yi magana kan lokacin da AI za ta zarce basirar ɗan Adam, saurin ci gaban fasaha a ƙasar Sin, dalilan da suka sa yake ƙara mayar da hankali kan Turai, da kuma rawar da ya taka a siyasa, inda ya amince cewa ya “ɗan tsunduma cikin harkokin siyasa fiye da yadda ya kamata.

“Sai dai Musk bai gabatar da wata hujja tabbatacciya da ke nuna cewa kuɗi za su daina zama masu muhimmanci nan da shekarar 2036 ba, kuma hasashensa na daga cikin ra’ayoyinsa game da makomar fasaha da tattalin arziki.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img