Ina da burin shiga Aljanna – Inji Sanata Karimi na Jam’iyyar APC

DA DUMI-DUMI

Sanatan Kogi ta Yamma, Sunday Steve Karimi, ya ce babban abin da ke sa yake fifita zaman lafiya shi ne burinsa na shiga Aljanna, yana mai jaddada cewa kowa zai tsaya gaban Allah domin ya ba da lissafin ayyukan da ya aikata a duniya.

Karimi ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da yake jawabi ga magoya bayansa bayan wata ganawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kogi ta Yamma.

Ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar tare da tabbatar da cewa APC ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2027.

“A rayuwata kullum ina son zaman lafiya ne saboda ina son na shiga Aljanna. Duk abin da mutum yake da shi a duniya na wucin gadi ne.

Ranar da za mu koma ga Allah, kowa za a yi masa hukunci bisa ayyukan da ya aikata,” in ji Karimi.

Sanatan ya bayyana cewa babban abin da APC ta sa a gaba shi ne tabbatar da sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027, yana mai kira ga ‘yan jam’iyyar da su manta da sabanin da ke tsakaninsu su haɗa kai domin cimma wannan buri.

Har ila yau, Karimi ya yabawa Shugaba Tinubu kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka wajen magance matsalolin tsaro, ciki har da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ‘yan bindiga.

Ya kuma ce shirin kafa ‘yan sandan jihohi (State Police) na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke nazari a kai domin ƙarfafa tsaro da yaƙi da masu aikata laifuka.

A ƙarshe, ya buƙaci dukkan mambobin APC a Kogi ta Yamma su kasance masu biyayya ga jam’iyyar, su guji rikice-rikice, tare da haɗa kai domin tabbatar da nasarar APC a babban zaɓen 2027.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img