An Hana Manyan Jami’an Trump Amfani da Motocin Haya Saboda Fargabar Harin Iran -Rahoto

DA DUMI-DUMI

Jami’an Trump Sun Guji Hawan Motocin Haya Saboda Barazanar Kashe Shi Daga Iran – WSJ

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an leƙen asirin Amurka sun shawarci wasu manyan masu ba Shugaba Donald Trump shawara da su daina amfani da motocin haya (car services), saboda fargabar yiwuwar Iran ta kai hare-haren kisan gilla a kansu.

Jaridar The Wall Street Journal (WSJ) ta ruwaito cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan hukumomin tsaro sun samu bayanan sirri da ke nuna yiwuwar Iran na ƙoƙarin kai hare-haren ramuwar gayya kan mutanen da ke da alaƙa da Trump.

Rahoton ya ce an umarci wasu daga cikin manyan mataimakan Trump su ƙara tsaurara matakan tsaro, tare da kauce wa zirga-zirgar da ka iya jefa rayuwarsu cikin haɗari.

Har zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga gwamnatin Iran da ta mayar da martani kan wannan rahoto.

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

Gwamnatin Najeriya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways Naira biliyan 18

Sai dai ya bayyana cewa gwamnati za ta biya kuɗin da aka tantance kuma aka tabbatar da shi, ba tare da ƙarin kuɗin da ya dace da hauhawar farashi na tsawon shekaru 20 ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img