Najeriya na neman sabon bashin dala biliyan 1.5 (Tiriliyan Biyu) daga Bankin Duniya

DA DUMI-DUMI

Najeriya na neman sabon bashin dala biliyan 1.5 (Tiriliyan Biyu) daga Bankin Duniya

Daga Wakiliya

Gwamnatin Najeriya a karkashin Bola Tinubu na neman sabon rancen dala biliyan 1.5 (kimanin Naira Tiriliyan Biyu) daga Bankin Duniya domin tallafa wa shirye-shiryen yaki da sauyin yanayi, kare al’umma da kuma bunkasa ci gaban yara kanana.

Bayanan gwamnatin Najeriya sun nuna cewa jimillar bashin da ake bin kasar ya kai naira tiriliyan 166.8, kwatankwacin dala biliyan 125.6, ya zuwa watan Yunin 2026.

Idan aka amince da sabon rancen, zai kara yawan bashin da ake bin Najeriya na cikin gida da na waje.

Bankin Duniya na daga cikin manyan cibiyoyin da ke bai wa Najeriya rance domin gudanar da shirye-shiryen raya kasa duk da cewa har yanzu yan kasar nan fama da tsadar rayuwa da talauci

- Advertisement -spot_img

Leave a Reply

- Advertisement -spot_img
Za ku so wadannan

BRAZIL: Mutumin da matarsa ta yanke wa azzakari zai sake aurenta

Yanzu haka, Gilberto na shirin sake aurenta, inda zai yi amfani da kuɗin diyya da ya samu bayan an yaɗa hotunan raunukan da ya samu a intanet ba tare da izininsa na yaɗawa ba.
- Advertisement -spot_img

Labarai masu alaka

- Advertisement -spot_img