‘Na Tara Kuɗi Na Sayi Kaya Daga China, Amma Da Na Karɓa Rabin Kayana Sun Bace’ – Hussaina Abdullahi
Wata ‘yar kasuwa, Hussaina Abdullahi, ta bayyana yadda ta yi asarar wasu daga cikin kayayyakin da ta shigo da su daga ƙasar China bayan shafe kusan watanni shida tana jiran a kawo mata su Najeriya.
A cewarta, ta tara kuɗaɗenta ne domin fara kasuwanci, inda ta sayi takalma da jakunkuna, sannan ‘yar uwarta da ke zaune a China ta shirya tare da tura kayan ta wani kamfanin jigilar kaya da ke Jihar Kano.
Hussaina ta ce duk da cewa jigilar irin wannan kaya kan ɗauki ƙasa da watanni biyu, nata ya ɗauki kusan watanni shida ba tare da ta samu damar bibiyar inda kayan suke ba.
Ta ƙara da cewa da kayan suka iso, kamfanin ya ƙara kuɗin jigilar daga Naira 51,000 zuwa Naira 89,000, tare da ƙin ba ta kayan har sai da ta biya ƙarin kuɗin.
Sai dai bayan ta karɓi kayan ta je gida ta fara buɗe su, ta ce ta tarar da cewa an rasa kayayyaki da dama. Wasu kwalayen takalman sneakers babu komai a cikinsu, yayin da jakunkuna da takalman loafer da dama suka ɓace.
A cewarta, ‘yar uwarta ce da kanta ta shirya kayan a China, don haka ta san adadin kayayyakin da aka turo. Ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin da suka ɓace ba a sayar da su guda-guda, sai dai a manyan haɗe-haɗe (bulk), lamarin da ya sa take zargin an buɗe kayan ne kafin su isa hannunta.
Hussaina ta ce ta tuntubi kamfanin jigilar kayan, inda suka ce ba su san abin da ya faru ba, amma sun yi alƙawarin za su bincika tare da dawo mata da bayani.
Ta bayyana cewa lamarin ya jawo mata asarar kuɗi, lokaci da kuma kawo cikas ga shirin da ta yi na fara kasuwancinta, tana mai cewa abin takaici ne kamfani ya kasa tabbatar da tsaron kayayyakin da aka ba shi amanar jigila.





